A wani mataki na kare ci gaba da yaɗuwar cutar korona ta Covid-19, kasar Chile ta ayyana dokar kulle a kasar dukda cewa an yi wa yan kasar sama da kashi 60 allurar rigafin ta korona.
Yo sai dai wannan doka an kafa ta me kawai a babban birnin kasar wato Santiago.
Yanzu haka wannan doka na nufin cewa kenan nutanen birnin da yawansu ya kai sama sa miliyan takwas za su ci gaba da zaman gida kenan daga ranar asabar har sai lokacin da aka tsagaita wannan doka.
A ranar Alhamis ne dai kasar ta sanar da cewa ana samun sabbin kamuwa da cutar korona kimanin 8000 ko wace rana, wanda galibinsu kuma mutane ne da suka gaza karɓar allurar rigafin cutar.
Hukumomin Lafiya sun ce wannan lamari ya ta’azzara karuwar rashin gadajen asibiti sakamakon tumbatsa da marasa lafiyar ke yi.
Kasar Chile na da rahotannin mutane kimanin miliyan biyu da suka harbu da cutar, yayin da sama da 30, 000 suka kwanta dama tunda daga bullowar cutar.