A yau Lahadi ne dubun-dubantar yan kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ke gudanar da zaben shugaban kasa duk da cewa babbar jam’iyyar adawar kasar ta kauracewa zaben wanda masu sukar lamirin ke ganin an fi bada fifiko ne ga Shugaba Dennis Sassou Nguesso.
Nguesso mai shekara 77 ana ganin ka iya galaba a kan zaben wanda zai doke abokan kararwar shi shida ciki har da wani masanin tattalin arziki kuma daya daga cikin wadanda suka fafata zaben a shekarar 2016 mai suna Guy-Brice Parfait Kolelas wanda a jiya asabar ya bayyana cewa yana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya.
Shugaba Dennis Sassou Nguesso wanda tsohon soja ne ya dare karagar5 mulki ne a shekarar 1979 inda ya shafe kimanin shekara talatin da shida kan karagar mulki, kuma hakan ya sanya shi wanda ya fi kowa ne shugaba dadewa kan karagar mulki.
A yanzu haka dai Kolelas shine kadai baban dan adawa da yake fafata zaben wanda ake ganin ana iya kai ruwa rana tsakanin shi da shugaba mai ci.