By Abbas Yakubu Yaura
Babban Kwamishinan kasar Ghana a Najeriya, Rashid Bawa, ya musanta rahotannin dake cewa kasarsa na cin zarafi da musgunawa ‘yan Najeriya da akayiwa gwajin cutar COVID-19.
Bawa ya nuna cewa yayin da gwajin cutar COVID-19 na PCR ya zama tilas, Ghana ba zata samar da sakamakon gwajin COVID-19 mai kyau ga baƙi ba.
Babban Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin daya ziyarci Shugaban Hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri, a Abuja ranar Talata kan zargin cin mutuncin wani dan Najeriya da aka yi wa gwajin cutar COVID-19 a Dubai, bayan ya isa Ghana.
Wani mai fasahar zane-zane dan Najeriya ya kuma ba da labarin yadda aka gaya masa a Ghana cewa yana da cutar COVID-19 ko da bayan gwajin rashin lafiya a wurin gwajin a Najeriya.
Suma ‘yan Najeriyar da suka fuskanci irin wannan hali sun koka da yadda aka kai su otal da karfin tsiya inda aka sanya su biya kusan Naira 500,000 na tsawon mako guda, yayin da ‘yan kasar Ghana da suka kamu da cutar aka kai su wani wuri killacewa kyauta.
Da yake jawabi game da zargin, Bawa, wanda Accra ta sake sabunta amincewarsa ga Najeriya, yace, “Ghana ba za ta samar da sakamakon gwajin cutar COVID-19 ga masu ziyara ba, musamman ‘yan Najeriya dake ziyartar Ghana.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A cewar wata sanarwa da Gabriel Odu na sashin hulda da jama’a da ladabi na NiDCOM ya fitar, wakilin ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake samun karuwar ‘yan matan Najeriya masu karancin shekaru da ake safarar su zuwa kasar Ghana, yana mai jaddada cewa ya kamata a yi duk mai yiwuwa wajen gurfanar da masu hannu da shuni da suka aikata wannan aika-aikar.
Jakadan ya amince da cewa, a baya-bayan nan kasashen biyu sun fuskanci wasu kalubale, duk da doguwar dangantakar dake tsakanin su.
“Daya daga cikin irin wadannan abubuwa shi ne yadda ake samun karuwar tashe-tashen hankula da suka shafi ‘yan kasuwar Najeriya a Ghana, wanda a cewar babban kwamishinan na Ghana; an cimma yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ministocin kasuwanci a Ghana da Najeriya. Har ila yau, an kafa rundunar hadin gwiwa da za ta kara sa ido kan lamarin.