Itopiya ta bayyana cewa, za ta gamsu matuka idan Turkiyya ta dauki nauyin shiga tsakaninta da Sudan don warware matsalolin kan iyaka da suke fuskanta.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Itopiya Dina Mufti ya yi jawabi a lokacin da ya ziyarci Turkiyya inda ya ce, ta hanyar diplomasiyya za a iya warware matsalar yankin Fashka da ya janyo rikici tsakanin kasarsa da Sudan.
Ya ce “Ba yaki muke son yi ba. Idan bangaren Turkiyya ya bayyana zai shiga tsakani, Itopiya za ta amince da wannan kokari.”
A ranar 15 ga Fabrairu Turkiyya da Itopiya suka gudanar da bukin cika shekaru 125 da kulla huldar jakadanci.
A ranar 15 ga Fabrairu Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu tare da na Itopiya Demeke Mekonnensuka bude sabon ofishin jakadancin Itopiya a Ankara Babban Birnin Turkiyya.