Ministan harkokin wajen kasar Hungary Peter Szijjarto ya yi Allah wadai sa bisa matakin da Kungiyar tarayyar turai ta EU ta dauka na nuna Fifiko wa Isra’ila kan Falasɗinawa.
EU ta bukaci bangarorin biyu da su tsagaita wuta, duk da cewa al’umma musulmi Falasɗinawa sunw ake ta kai wa hare haren.
Peter Szijjarto ya ce ya sha mamaki matuka bisa ganin yadda EU ta nuna karara cewa ba ta tare da gaskiya cikin wannan lamari duk da irin musgunawa da yahudawan Isra’ila ke yi wa Falasɗinawan.
A Jiy ne Jami’i mai kula da harkokin kasashen waje na kungiyar tarayyar turan Josep Borrel ya fitar da wata sanarwa mai nuna cewa ya kamata Falasɗinawa su takaita takalar mutane.
Ruwa Bama-bamai da rokoki da Isra’ila ke yi kan Falasɗinawar ya yi sanadiyar rasa rayukan Mutane da dama a jiya kawai, banda wadanda suka rigaye mu gidan gaskiya tun da fari kama daga farko yakin kimanin mako guda kenan.