Fira Ministan kasar Indiya Narendra Modi a ranar Juma’a ya ba da sanarwar cewa za a soke dokar noma guda uku da ta haifar da zanga-zangar shekara guda da manoman Indiya suka yi.
Sanarwar ta zo ne gabanin manyan zabukan jihohi da suka hadar da Uttar Pradesh da Punjab, wadanda ke matsayin gida ga manyan al’ummomin da suke noma a Indiya.
Kungiyoyin manoma sun fara gudanar da zanga-zanga tun a watan Nuwamba 2020 domin neman a janye dokar noma da gwamnati ta ce ana bukatar su don zamanantar da harkar noma.
Dokokin na da nufin sassauta ka’idoji game da adanawa da sayar da amfanin gona, kuma manoma na fargabar manyan kamfanoni ne kawai za su amfana yayin da manoma za su kasance cikin jimami na kasuwa mai ‘yanci.
A wani jawabi na bazata ga al’ummar kasar, Modi ya ce an yi dokar ne don karfafawaa kananan manoma. “Wani sashe ne kawai daga cikinsu ke adawa da dokokin, amma mun cigaba da kokarin ilmantar da su akai,” in ji shi.
Modi ya ce gwamnati ta gaza shawo kan wani bangare na manoman don fahimtar amfanin wannan doka kuma za a soke dokar a zaman majalisar.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito cewa wannan gagarumin sauyi dai ya zo ne a matsayin wani tallafi ga manoman da ke zanga-zangar, wadanda dubbansu suka yi taru a kan manyan titin babban birnin kasar tun shekaran jiya.
Deepak Lamba, shugaban kungiyar Jai Kisan Andolan, a dandalin manoma masu zanga-zangar ya ce sanarwar nasara ce ga manoma. “Wannan babbar nasara ce ga manoma, ganin rashin kyakykyawan fatan da suke da shi a zabuka masu zuwa saboda wadannan dokoki, gwamnati ta fahimta ta janye su,” in ji Lamba.