By Abbas Yakubu Yaura
Kasar Masar ta rufe tashoshin jiragen ruwan ta takwas saboda rashin kyawun yanayi, kamar yadda jami’ai suka bayyana a ranar Litinin.
Hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta Red Sea tace an rufe tashoshin jiragen ruwa na Port Tawfiq, El-Zayteyat da Sharm El Sheikh da sanyin safiyar ranar Litinin.
An kuma rufe tashoshin jiragen ruwa na Adabiya, Ain Sokhna, Port Said ta yamma, Port Said ta gabas da Al Arish daga baya a ranar Litinin, in ji wata sanarwa daga Babbar Hukumar Kula da Tattalin Arziki na Canal Suez.
Sanarwar ta kara da cewa ana sa ran sake bude tashoshin jiragen ruwa da zarar yanayi ya inganta.
A halin da ake ciki kogin Suez Canal ya sami mafi girman kudaden shiga a cikin watan Nuwamba, inda ya kawo dala miliyan 571.3, a cewar shugaban hukumar kula da hanyar ruwan.
Shugaban hukumar kula da tashar ruwa ta Suez, Osama Rabie, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa magudanar ruwan ta kuma samu mafi girma a kowanne wata da tan miliyan 113.5.
Rabe yace goyon bayan shugabannin siyasa ya yi matukar tasiri wajen cimma manufofin ci gaban hukumar.
Ya kara da cewa hukumar na duba yiwuwar karfafa wa jiragen ruwa dake aiki da iskar gas, da kuma tattauna hanyoyin da za a yi amfani da makamashin da za a iya sabuntawa a tashoshin jiragen sama da na ruwa da dama.
Mashigin ruwa na Suez yana da kusan nisan kilomita 200, kuma kusan kashi 12 cikin 100 na kasuwancin duniya – ciki har da ganga miliyan 1 na mai – suna ratsawa ne ta cikin ruwan kowace rana.
Kimanin kashi 12% na kasuwancin duniya, kusan ganga miliyan daya na mai da kuma kusan kashi 8 na iskar gas na masu ruwa da tsaki suna ratsa magudanar ruwa kowace rana.