Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumomin kasar Mexico a ranar Asabar din data gabata sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a wani harbe-harbe da aka yi tsakanin wasu ’yan daba a gabar teku dake kusa da wurin shakatawa na Cancun dake yankin Caribbean, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu.
Rikicin dauke da makamai, wanda ya faru a ranar Alhamis, shi ne karo na biyu daya girgiza Riviera Maya na Mexico a cikin ‘yan makonnin nan kuma wani rauni ne ga masana’antar yawon shakatawa dake murmurewa daga barkewar cutar Corona.
Ofishin babban mai shigar da kara na jihar Quintana Roo dake gabashin kasar yace ya yi nasarar gano uku daga cikin motoci hudu da ake zargin masu harbin ne suka yi tafiya dasu zuwa gabar teku. Sun kama wasu mutane biyu dake tuki, yayin da daya ya yi nasarar tserewa
“An kama direbobi biyu yayin da na uku ya gudu, kuma an yi musayar wuta da jami’an ‘yan sanda, inda suka yi nasarar tserewa zuwa wani daji,” in ji babban lauyan a wata sanarwa.Har ila yau, ofishin yace binciken farko ya nuna cewa kungiyoyin dake da hannu a wannan rana sun rabu da kungiyar ta Sinaloa wadanda ” ke takaddama kan yankin wajen sayar da kwayoyi.”
Harbin da aka yi a ranar 4 ga watan Nuwamba ya faru ne a bakin teku a wajen daya daga cikin otal-otal na alfarma da ke kusa da Cancun, wani shahararren wurin yawon bude ido.sai dai kuma Hukumomin yankin sun ce fadan ya kasance ne tsakanin gungun ‘yan kungiyar dillalan miyagun kwayoyi.
Kasar Mekziko dai na fama da zubar da jini mai alaka da kungiyar ‘yan banga da aka kashe sama da mutane 300,000 tun bayan da gwamnati ta tura sojoji a yakin da ake sayar da miyagun kwayoyi a shekara ta 2006.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a watan da ya gabata ma sai da wasu ‘yan yawon bude ido biyu daga Jamus da Indiya suka mutu a wani artabu tsakanin wasu da ake zargin masu sana’ar sayar da muggan kwayoyi ne a Tulum, yayin da wasu da dama suka samu raunuka, har’ila yau a cikin shekarar 2017, wasu ‘yan kasashen waje uku sun mutu a cikin mutane biyar a wani harbi da aka yi a wani bikin kade-kade na lantarki a Playa del Carmen.
Kazalika Abubuwan da suka faru sun sa kasashen Turai da Amurka gargadin ‘yan kasarsu game da hadarin dake tattare da ziyartar yankin Caribbean na Mexico, daga cikin manyan wuraren bakin teku na duniya. Yawon shakatawa yana wakiltar kashi 8.5 na yawan amfanin gida na Mexico kuma shine babban tattalin arziki a yankin kudu maso gabas. wanda ya hada da Riviera Maya.