A ci gaba da yin adawa da juyin mulkin da aka yi a kasar Myanmar, birni mafi girma a kasar, Yangon, ya shaida wata sabuwar zanga-zanga a safiyar wannan Litinin.
Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun fantsama ne biyo bayan toshe shafukan intanet da sojojin Myanmar suka a jiya da daddare.
Wannan na zuwa ne a yayin da lauyan hambararriyar shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi ya ce an mayar da tsohuwar shugabar inda sojoji ke tsare da ita har zuwa ranar Laraba inda ke sa ran kotu za ta saurari shari’ar sako Suu Kyi din da aka kai gabanta.