Ministan Mai Chief Timpre Sylva, ya yabawa kasar Sengal kan neman kasar Nigeria ta taimaka mata domin samar da kamfanoni Mai da iskar gas a kasar. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Chief Timpre Sylva, ya bayyana hakane a lokacin da yake karbar bakuncin Minsita Aissitou Sophie Gladima ta kasar Sengal tare da makarrabanta a garin Abuja, a yau Litinin.
Yace daman ya kamata kasashen Africa su zo su hada kansu domin dogaro da kai, su rage yawan dogaro da kasashen turawa wajan neman taimako.
KARANTA:- Rijistaran hukumar Jamb ya sauka bayan wa’adinsa ya kare
Chief Timpre Sylva, ya cigaba da cewa, kasar Nigeria nada dama da yawa a matsayin ta na Kasa data mallaki man fetur da iskar gas, tun dogon lokacin da dadewa da yawuce kasar ta samu dabaru daban-daban da kuma matsaloli daban-daban.
Yace an dai fara samar da man fetur a kasar Nigeria tun shekarar 1937, inda aka fara kasuwancinsa a shekarar 1950, yace kasuwancin man Fetur ya fara karfi a shekarar 1956, inda jirgin ruwa na farko da ya fita da man fetur a kasar Nigeria a 1958.
“Wannan shike nuna cewar, kasar Nigeria ta share shekaru sittin tana samar da man fetur, inda an sami dabarori da dama a tsakanin lokacin.”
“A dai lokacin da aka fara samar da man fetur a Nigeria mudai kawai Yan kallo ne, da yawancin ma’aikatan duk bakin haure ne, gaba dayan Mutanen mu sun zama Yan kallo, amman daga baya abubuwan sun sauya.”
“Hakika wanna babbar cigaba ne a kasar Nigeria, wanda a halin yanzu kaso mafi yawa na samar da man fetur, Kamfanonin Nigeria ke samar dashi.”
Yace “daga cikin amfanin samar da man fetur da iskar gas a kasa, shine wadata kasa da kudade.
Ya Kuma yi alkawarin cewar kasar Nigeria za ta tallafawa kasar Senegal ta fara samar da man fetur da iskar gas na kanta, domin ta shiga cikin jerin kasashen dake samar da man fetur ta duniya watau (APPO).
A lokacin da take jawabi, Minista Gladima ta kasar Senegal, ta yabawa Ministan kan irin tarbar da yayi mata, inda tace kasar Senegal za ta cigaba da kulla kawance da Nigeria domin ta koya daga gareta.
Tace tana sha’awar kasar Nigeria ta tallafawa Senegal a fannoni guda hudu a wajan samar da kamfanonin dakan samar da man fetur da iskar gas.
Ministan ta nuna sha’awar na shiga cikin jerin kasashen dake samar da man fetur da iskar gas ta duniya watau (APPO).
Comments 1