Marcelino Ansorena, Jakadan kasar Sipaniya a Nijeriya, ya tabbatar da cewa; kasar sa za ta muhimmantar da zuba hannun jari a Nijeriya domin bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu.
Ansorena ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai a wani taron rawa na Sipaniya mai taken “Alguien vendrá a buscarnos” da ya gudana a daren Juma’a a Abuja.
Taron dai Ofishin Jakadancin Sipaniya a Nijeriya ya shirya shi, wanda aka saba shiryawa a duk shekara domin bunkasa al’adun kasashen Nijeriya da Sipnaiya.
Ya bayyana cewa Nijeriya da Sipaniya suna da alaka ta fannoni daban-daban wanda ya hada da man fetur da iskar gasa, sannan ya ce hatta matsalar tsaron kasashen iri guda ne. Ya ce kuma samar da tsaron Nijeriya yana daga cikin fatan su.
Ya ce suna da sha’awar zuba hannun jari a bangaren fina-finan Nijeriya, kuma za su bai wa bangaren muhimmanci.