Gidan talabijin na Al Jazeera ta bayyana cewa kasar Sudan ta soke lasisin Al Jazeera Mubasher, wani bangare na cibiyar sadarwa da ke Qatar.
Hukumomin sun zargi gidan talabijin din da watsa shirye-shiryen talabijin na ”marasa kwarewa” game da haifar da zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi.
“Hukumomin Sudan sun sanar da soke amincewar Al Jazeera Mubasher tare da hana tawagarta yin aiki a Sudan,” in ji tashar ta twitter.
Sudan dai ta fada cikin rudanin siyasa tun bayan da babban hafsan sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kaddamar da juyin mulki a ranar 25 ga watan Oktoba.
Juyin mulkin da sojoji suka yi ya janyo zanga-zangar neman mulkin farar hula. Sojoji sun mayar da martani da kakkausar murya.
Akalla masu zanga-zangar 64 ne aka kashe, a cewar masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya, kuma wani dan sanda shi ma ya rasa ransa.
Al Jazeera ta bayyana hakan a karshen makon da ya gabata, ta kuma ce ba da fitattun labarai game da zanga-zangar kuma a karshen shekarar da ta gabata ma ta watsa wata hira da Burhan.
A watan Nuwamba, kwanaki bayan tattaunawar, ta ce an kama shugaban ofishinta na Khartoum Al-Musalami al-Kabbashi a gidansa.
Babban editan jaridar sojojin kasar Ibrahim al-Hory daga baya ya zargi Kabbashi da buga bayanan “karya” da kuma yada “tsoffin faifan bidiyo… wadanda suka haifar da rikici” a kasar.