By Abbas Yakubu Yaura
Kasar Turkiyya ta yi marhabin da matakin da Najeriya ta dauka na sayen jiragen ruwa daga tashar jiragen ruwanta, saboda la’akari da yadda take kara karfi a duniya a matsayinta na karfin soji data samu gagarumar nasara a kasashen Iraki da Siriya da Libiya da kuma kasar Azarbaijan ta baya-bayan nan.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da shugabannin biyu sukayi a ranar juma’ar da shugaban kasar, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) kafin a fara taron hadin gwiwa na kasar Turkiyya da Afirka karo na 3.
Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar mai take, ‘Nigeria, Turkey don karfafa harkokin tsaro, ’.
An ruwaito Erdogan na cewa ana ci gaba da tattaunawa kan yadda za a karfafa karfin masana’antun tsaro dake Kaduna bisa yarjejeniyar da aka kulla a ziyararsa ta karshe a Najeriya.
A nasa bangaren, shugaba Buhari yace a ci gaba da kokarin tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya, kasar za ta hada kai da Jamhuriyar Turkiyya wajen tinkarar kalubalen tsaro da take fuskantar ta.
Wannan shi ne kamar yadda yace Turkiyya na da kwarewa a aikace wajen tunkarar kalubale a tsawon shekaru kuma Najeriya ta ci gajiyar hakan.
Shugaga Buhari ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a birnin Istanbul a taron kasashen biyu da ya yi da takwaransa na Turkiyya, Recep Erdogan, jim kadan kafin a fara taron hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka karo na 3.
Buhari, wanda ya amince da cewa kasar Turkiyya ta samu kwarewa sosai wajen tunkarar kalubalen tsaro iri daban-daban, sannan yace Najeriya za ta ci gaba da bin wannan kwarewa.
Da yake ba da tabbacin alakar dake tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da bunkasa domin moriyar juna, shugaban yace ya ji dadin irin tallafin da Turkiyya ke baiwa Najeriya a fannin tsaro da zaman lafiya.
Buhari ya shaida wa mai masaukin baki cewa, “Ina so in nuna farin cikina da gayyata ta musamman ga wannan taro da kuma nuna farin cikina da tallafin da kuke yi na tunkarar kalubalen dake gabanmu.
Erdogan yace, “Turkiyya ta fahimci kalubalen da Najeriya ke fuskanta da kuma bukatunta, kuma a shirye muke mu taimaka muku wajen biyan wadannan bukatun musamman a fannin tsaro.
“Na yi farin ciki da cewa Najeriya na kara yin hadin gwiwa da sauran kasashe a fannin tsaro da kiwon lafiya, kuma a shirye muke mu ba ku hadin kai a wannan fanni da sauransu.”