By Abbas Yakubu Yaura
Kasar Uganda ta tuhumi mutane 15 da suka hada da wata mace mai juna biyu da laifin ta’addanci, bisa zarginsu da hannu a hare-haren baya-bayan nan da ake zargin wata kungiyar ‘yan tawaye da kaiwa, in ji ‘yan sanda a yau Juma’a.
Kasar ta Uganda dai ta fuskanci hare-haren bama-bamai a watan Oktoba da Nuwamba wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.
Hukumomin Uganda sun ce wata kungiyar ta’addanci ta cikin gida dake da alaka da kungiyar (ADF) wata kungiyar ‘yan bindiga da Washington ta alakanta da kungiyar IS – ita ce ke da alhakin kai hare-haren.
“Mutane 15 ne suka gurfana a gaban kotu jiya bisa zargin ta’addanci, taimakawa,wajen tallafawa ta’addanci da kuma zama kungiyar ‘yan ta’adda,” in ji mataimakin kakakin ‘yan sandan birnin Kampala, Luke Owoyesigyire, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran faransa AFP a yau Juma’a.
Bayan kai hare-haren, kasar Ugandan a watan daya gabata ta jibge sojoji tare da kaddamar da hare-hare ta sama a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) kan kungiyar ADF, bayan da Kinshasa ta bai wa Kampala izinin bin sahun masu fafutuka a kasarta.
Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a ranar 16 ga watan Nuwamba a Kampala babban birnin kasar, ya yi sanadin mutuwar mutane hudu tare da jikkata 33.
Hare-haren da kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa, sun biyo bayan harin bam da aka kai a wani wurin cin abinci a gefen titi a ranar 23 ga watan Oktoba wanda ya yi sanadiyar mutuwar mace guda, da kuma wani harin kunar bakin wake da aka kai a wata motar safa a kusa da birnin Kampala a ranar 25 ga watan Oktoba wanda ya raunata mutane da dama.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Owoyesigyire ya ce dukkan wadanda ake zargi 15 na da hannu a hare-haren bam guda hudu kuma za a ci gaba da tsare su har zuwa ranar 13 ga watan Janairu inda za su sake gurfana a gaban kotu.
Tun daga watan Afrilun shekarar 2019, wasu hare-haren ADF a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango kungiyar IS ne ke daukar alhakin kai harin, wanda ke bayyana kungiyar a matsayin reshenta na lardin tsakiyar Afirka.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A cikin watan Maris, Amurka ta sanya ADF a cikin jerin kungiyoyin ” ‘yan ta’adda” masu alaka da IS.
Uganda ta kuma zargi kungiyar da kai harin bam a cikin watan Agusta a kan jana’izar kwamandan sojojin da suka jagoranci wani gagarumin farmaki kan mayakan Al-Shabaab a Somaliya.