Kamfanin Shafin Sada zumuntar nan na zamani Facebook ya rariƙe asusun shafin na facebook mallakin Shugaban kasar Venezuela Niçolas Maduro biyo bayan ikirarin da wallafa a shafin nashi cewa magungunan gargajiya za su iya warkar da cutar annobar Covid-19.
Tun a watan Janairu ne dai Maduro ya wallafa wannan batu nashi inda ya ce akwai ganyayyaki masu daraja da su magance cutar, to amma tun bayan wanchan lokacin bai kara samu damar sake wallafa wani abu a shafin nashi ba.
Kamfanin Facebook ya ce ba sau ɗaya ba ba biyu ba Shugaban Kasar ya saba ka’aida da dokokin sa bisa wallafa abubuwa dake kawo ruɗani.
To sai dai ba Mista Maduro ne shugaba na farko da fuskanci fushin kamfanin na Facebook kan wallafa bayanai da suka shafi cutar ta Covid-19.
Tsohon Shugaban Kasar Amurka ma dai Donald Trump da na Brazil Jair Bolsonaro dukkannin su sun ɗanɗana Kuɗar su bisa irin matakin Maduro.