Akalla kasashen Afrika goma Sha Bakwai ne suka kauracewa kada kuri’ar Allah Wadai da mamayar Rasha a Ukraine a yayin babban taron majalissar Dinkin duniya
Kasashen sun hada da: Afrika ta Kudu, Algeriya, Uganda, Burundi, Senegal, Sudan ta Kudu, Mali da kuma Muzambique.
Sauran sun hada da : Sundan, Namibia, Angola, Zimbabwe, Equatorial Guinea, da dai sauran su.
Yayin da yake bayyana dalilin kasarsa na kin kada kuri’ar, Wakilin Uganda Adonia Ayebare ya ce, Sun yi hakan ne domin tsayawa “a tsaka-tsaki”, a matsayin su na kasa Mai jagoranci Yan baruwanmu.
Kungiyar N.A.M ta kunshi kasashe masu tasowa gone guda 120, domin tabbatar da ‘yancin kansu daga da’awar da manyan kasashen duniya biyu ke yi.