Shugabannin kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arziki sun amince da mafi karancin haraji na duniya na kashi 15 a kan manyan masu kasuwancin kasa da kasa.
Za su yi amfani da sabbin dokokin a hukumance a ci gaba da taron da kasashen G20 ke yi a birnin Rome yau Lahadi.
Joe Biden, shugaban Amurka wanda ke babban birnin Italiya don tattaunawa, ya yaba da yarjejeniyar haraji a matsayin “wata almara”.
Dokokin haraji, wani bangare ne na shirin garambawul da kasashe kusan 140 suka sanyawa hannu, wanda zai sa ya yi wahala ga kamfanoni na kasa da kasa – wadanda suka hada da kamfanin Google, Amazon, Facebook, Microsoft da Apple kuma hakan zai yi tasiri wajen sanyawa su guje wa haraji ta hanyar kafa ofisoshi a kananan hukumomin haraji.
Kazalika dokokin za su yi niyyar kawo karshen gasar harajin da aka shafe shekaru da dama ana yi tsakanin gwamnatoci domin jawo jarin kasashen waje.
Sakatariyar baitul malin Amurka Janet Yellen ta yaba da amincewar da G20 ta yi na yarjejeniyar haraji a matsayin “mai tarihi” yayin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kira shi “babban nasara”.