Kungiyar kasashen da suka fi akarfin tattalin arzikin a duniya wato G7, ta yi alkawarin taimaka wa gwamnatin tarayya da kudin da zatayi amfani da su, wajan magance matsalar yunwa.
Jaridar The Cable ruwaito cewa, wadannan kasashen 7, sun sha alwashi bada gudumawar Dala miliyan 382, domin a kawo karshen karancin abinci a fadin Nijeriya baki daya.
Kasashen sun bayyana hakan ne a wajan taron su na kaddamar da shirin “G7 Famine Prevention Compact Launch” da ya gudana a jiya ranar Alhamis, 8 ga watan Yulin, shekarar 2021 da muke ciki.
Za ayi amfani da wannan makudan kudi ne, a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda mutane su ke cikin mawuyacin hali, a dalilin hare-hare kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram.
Kasashen masu karfin tattalin arzikin wato G7, sun hada da; Amurka, Birtaniya, Kanada, Faransa, Jamus, Italiya da Jafan
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari yayi Allah Wadai da harin da aka kai a Adamawa
Idan za’a kwatanta darajar kudaden da kasashen zasu bai wa Nijeriya, da kudin Naira ta gida, kudin zai kai kimanin Naira biliyan dari da tsassa’in.
Jakadiyar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta karanto jawabi a madadin kasashen, inda ta ce, sun ware wa kasashe 42 gudumuwar Dala biliyan bakwai.