Manyan ƙasashen duniya masu arzikin man fetur sun amince su kara yawan man da suke hakowa.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa wannan mataki nasu na a wani yunkuri na taimakawa wajen saukaka tsadar kayayyaki.
Mambobin kungiyar masu arzikin man fetur ta OPEC, wadanda suka haɗar da Rasha – sun amince a ranar Laraba don kara yawan ganga 100,000 a kowace rana a kasuwa daga watan Satumba.
Matakin dai ya kasance cin fuska ga shugabannin da suka yi kira da a kara kaimi wajen samar da kayayyaki.
Sun hada da shugaban kasar Amurka Joe Biden, wanda ya je Saudiyya a wani yunkuri na shawo kan kasar da ta kara hako mai don taimakawa wajen kwantar da farashin.
An ci gaba da cinikin danyen mai a kan fiye da dala 100 tun daga watan Fabrairu, abin da ya kara tsadar rayuwa a kasashe da dama.
Kungiyar ta Opec mai mambobi 13, an kafa ta ne a shekarar 1960 a matsayin kungiya mai zaman kanta, da nufin daidaita yawan man da ake samu a duniya da kuma farashinsa.
Saudiyya ita ce babbar mai samarwa da abun bukata a cikin ƙungiyar kuma bayan ganawa da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed Bin Salman, Shugaba Biden ya ce yana sa ran za a kara yawan man da ake samarwa a kasar.
A watan Yuli da Agusta, Opec ta amince da kara sama da ganga 600,000 a kasuwar kowace rana.