Kasashen Turai na kokarin kasance wa cikn shiri yayin da kasar Rasha ke cigaba da barazanar toshe bututun gas din da take baiwa kasashen. Kamar yadda kafar yada labarai ta DW ta ruwaito.
A cikin wannan yunkun dai na kasashen sun lashi takobin taimakawa juna domin magance kalobalen da zasu fuskanta dangane da matakin na Rasha.
Jaridar Bloomberg A jiya litinin ta ruwato cewa, kasar Ukraine tace, tana sa ran zata fitar da kayayyakin abinci a karo farko karkashin yarjejeniyar da majalisar Dinkin Duniya ta goyi baya , inda Rasha zata bude kogin Black Sea da ta toshe.
Wannan na zuwane a daidai lokacin da harin da Rasha ta kai da makai masu linzami ke kawo shakku kan wannan yarjejeniya.
Shirya Fitar da kayyakin zai cigaba a karon farko tun bayan da Rasha ta fara mamayar makwabciyar ta Ukraine watanni biyar da suka gabata.
Sai dai Babban kamfanin gas din Rasha ya kara haifar da damuwa bayan da yace zai sake kaste fitar da man gas dinta zuwa nahiyar Turai.
A ranar Juma’a ne Gwamnatocin kyiv da Moscow suka amince da wannan yarjejeniya domin fitar da miliyoyin buhuhuwan alkama da sauran kayayyakin abinci da aka tara a tekun Black sea, a wani yunkuri na magance matsalar abinci da kasashen duniya ke fuskanta.
Kasa da awa 24 da wannan sanarwar Mascow takai hari a Odessa daya daga cikin wuraren fitar kayyakin da ke cikin yarjejeniyar, lamarin da ya haifar da damuwar ko Kremilin ba zata mutunta wannan yarjejeniyar ba.
Sai dai duk da hakan , Ministan harkokin more rayuwa Oleksandr Kubrakov wanda shine ya jagoranci tawagar ta Ukraine wurin sasantawa da kullar yarjejeniyar a makon da ya gabata , yace suna sa ran yarjejeniyar zata fara aiki nan bada jimawa ba.
Jami’yan Ukraine sunce mashigin ruwan Chornomorsk dake Kudancin Kasar ne zai zamo na farko cikin wadanda za abude, inda yake jadda muhimmanci tsaro bayan wannan harin da aka kai a yankin Odessa.
Duk da haka, Kubrakov ya ce, karkashin yarjejeniyar za a gudanar da hakar ma’adinai na musamman a cikin hanyoyin jigilar kayayyaki da ake bukata don fitar da hatsi, yayin da jiragen ruwan Ukraine za su raka ayarin motocin da za su yi jigilar hatsi har ma da takin zamani
A wata sanarwa da ya fitar bayan tattaunawa da Kubrakov ta wayar tarho, Ministan Tsaron Turkiyya Hulusi Akar , ya yi maraba da kudurin na Ukraine na dawo da jigilar kayayyaki, yana mai cewa, abune mai muhimmanci jirgin farko ya fara tashi daga wuraren da aka amince
Kasashen Ukraine da Rasha dai sun kasance manyan kasashen da sukafi fitar da kayayyakin abinci a duniya , amma mamayar da Rasha ke yi a duniya ya kawo ma Ukraine tarnaki wurin fitar alkama saboda rufe tashoshin jiragen ruwa sanadiyar yakin.
A cikinA tsawon wannan lokacin , kulle tashoshin jiragen ruwa da sojojin Rasha suka yi ya haifar da tashin farashin kayayyakin abinci a fadin duniya, inda aka yi ta nuna fargabar samun matsalar yunwa, bayan da lamarin ya bar kimanin ton miliyan 25 na alkama da sauran kayayyakin abinci makale a Ukraine.
Kazalkka Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky Ya ƙiyasta cewa zasu fitar da kayyakin abinci da kudin su zai kai aƙalla dalar Amurka Biliyan 10, karkashin yarjejeniyar.