Hukumar bada agajin gaggawa Red Cross a Nigeria reshen jihar Fulato wato , ta yi kira ga al’uma baki daya, da su bada tataimakon Jini ga wadanda harin Yan bindiga a Yelwa Zangam dake karamar hukumar Jos ta Arewa ya shafa a daren ranar Talatar data gabata.,
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, an sami karancin Jini a asibitin Gwamnati dake fadin jihar.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, haryanzu ba’asami adadin yawan jinin da ake bukata ba, domin sanya wa wadanda suka sami raunika sanadiyar harin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun farmaki motar kudi, sun kashe Dan sanda guda a Ondo
Shugaban sashin sadar wa na hukumar ta Red Cross a Nigeria Mafeng Mark, a cikin wani sakon sa ta kafar sada zumunta na whatsApp , ya bukaci Al’uma da kuma yan kasa nagari, da su taimaka wa wadanda suka sami raunika sanadiyar harin, kuma aka kwantar da su asibitocin dake fadin jihar, domin ceto rayuwar su.
Sakon ya nuna cewa ” Hukumar Red Cross a Nigeria shiyar Fulato na rokon al’uma baki daya, da su taimaka wa wadanda harin kwana-kwana nan ya rutsa da su da Jini” inji shi.
“Sabida lamari na gaggawa muna rokonku da kuziyar ci asibiti na Musamman dake Fulato domin taimako da kowani irin nau’in Jini.”