Femi Fani-Kayode, Tsohon Ministan Sufuri, kuma Ɗan Jam’iyyar APC yace bazai ƙara yin shiru ba, saboda siyasa, ya cigaba da Kallon kashe-kashe yana faruwa a Ƙasar.
Fani-Kayode a cikin jawaban daya fitar a Shafin Twita a daren ranar Alhamis, yace ƴan Najeriya da wadanda ke saman Mulki na binshi bashin faɗin gaskiya komin ɗacin ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari bai taɓa Katsalandan ba a Harkokin Shari’a — Inji Babban Jojin Najeriya
Tsohon Ministan Wasannin wanda yana ɗaya daga cikin masu yawan caccakar wannan Gwamnati ta yanzu, kafin ya shiga Jam’iyyar, yana maida jawabi ne akan kisan ƙare dangi a Benue da Jahar Filato.
Yace Gwamnatin Buhari an bar Gwamnatin Buhari da ƴan watanni ta kawo ƙarshen matsalar tsaro, akan abinda ya bayyana “hauka” tare da daina kisan Al’umma haka nan.
Tsohon Jigon Jam’iyyar PDP yace dole Gwamnati ta gano wata hanya da zata kawo ƙarshen wannan kisan ƙare dangi, wahalhalu akan Al’ummar Ƙasa kafin barin Ofis.
“A yau dole mu ajiye siyasa a gefe, mu faɗi gaskiya komin ɗacin ta. An kashe mutane 100 a Filato, tare da yanka mutane 25 a Benue. Wannan abun kunya, abun baƙin ciki, kuma abinda baza’a yarda dashi ba,” inji shi.
Tsohon Ministan ya bayyana mamakin sa na tsawon wane lokaci za’a kawo ƙarshen wannan kisan, garkuwa da mutane, a yayin da Gwamnati sai dai kawai ta bada sanarwar jaje.
Fani-Kayode ya bayyana damuwar sa na adadin ƴan Najeriya nawa zasu mutu kafin ƴan Ƙasar su hankalta.