Almajiran Malam Ibraheem Zakzaky, wadanda suke bin tafarkin mazhabin shi’a sun koka tare da Allah-wadai ganin yadda ake Kashe-kashen mutane a Arewacin Nijeriya tsawon lokaci wanda hakan yasa mutane da daman gaske ke yin hijira daga garuruwansu zuwa wasu kauyukan, wadanda ke kashe-kashen ke bin wadanda ba su gudu ba su kashe su ba tare da wani kwakkwarar Hujja ba kamar yadda ‘yan shi’ar suka bayyana.
Sun bayyana hakan ne a wata sanarwar manema labarai wanda daya daga cikin almajiran kungiyar, Abdullahi Muhammad Musa ya fitar a madadin dandalin Dalibai na Academic Forum, inda suka nuna matukar damuwarsu ganin yanda ake kashe-kashen ba tare da gwamnatin ta dauki wani mataki ba; “kullum sai dai a yi ta gafara babu karo.” Inji su. Inda suka kara da cewa; “wannan kashe-kashen da ake yi wani abu ne da aka tsara za a yi tun tsawon shekaru kamar yadda Jagoranmu Shaikh Al-Zakzaky ya sha bayyanawa.” inji Abdullahi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; “A Shekarar 2013, Sheikh ya sanar a wani Jawabin da ya mana cewar, lallai zinare da abubuwan arziki za su zo diba a yankin Arewacin Nijeriya, tun daga Kaduna har Zamfara Zinare a kwance jagoranmu ya bayyana hakan, ya tona asirin makircinsu, kuma jagoranmu ya bayyana za su yi amfani da ta’addanci ne wajen korar mutane a wannan yankin tun tsawon shekaru, gashi kuma yanzu ana yi.”
Abdullahi ya kara da cewar; “tona Asirin ta’addancin da ake shirin yi a Nijeriya ne da jagoranmu yake fada kullum ya sa suka dira gidansa suka kashe ‘yan’uwanmu sama da dubu kuma suka tsare Malaminmu da raunuka a jikinsa, kuma zamu ci gaba da Neman ‘yancinmu har mutuwarmu akan wannan zaluncin da aka mana.” Ya tabbatar.