Wasu matasa a jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya sun barke da zanga-zangar lumana inda suke kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari ya gaggauta shawo kan matsalar tsaro da take addabar wannan yankin arewa,
Sun kuma jaddada bukatar da yake akwai na cewa; idan kuma ba zai iya ba to ya yi gaggawar sauka daga mukaminsa na shugaban kasar.
Zanga-zangar da ake gudanarwa a jihar Kaduna akwai barazanar cewa za ta fantsama a sauran sassan jihohin Nijeriya musamman arewacin kasar inda matsalar tsaron tafi kamari.