Kashe-Kashe: Ku daina ta’addancin nan, CAN ta gargaɗi IPOB
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya a ranar Laraba tayi kira ga Shuwagabancin Ƙungiyar Ƴan ta’addan Biafra dasu daina ta’addancin da suke yi da kashe kashe domin neman Ƙasar su.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Jibge Jami’an tsaro a wurin Zaɓen Fidda Gwanin PDP na Lagos
Ƙungiyar ta kuma yi Allah Wadai da babbar murya na kisan Fatima da ƴaƴan ya guda 4 daga ƴan IPOB.
Kungiyar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da Fasto Adebayo Oladeji, Babban Mai Taimakawa Shugaban CAN Rabaran Dr Samson Ayokunle.
CAN ta buƙaci ayi adalci ga Fatima da iyalan ta, tana mai kira ga Shuwagabannin tsaro dasu gano waɗanda suke gudanar da wannan mummunan lamari domin kiyaye Kashe-kashe a Ƙasar.
Sanarwar tace “wannan ta’addancin ba zamu yarda dashi ba ga CAN da duk wani mai hankali. Muna kira ga Hukumomin tsaro.