An kashe akalla Mutane uku a wani sabon hari a kauyuka biyu dake karamar hukumar Bassa na Jihar Filato.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an Kai sabbin harin ne a wasu kauyuka biyu mabanbanta dake karamar hukumar.
An Kai farmaki na farko ne a yammacin jiya Lahadi a yankin Kwachudu, inda aka fille kan Makiyaya Fulani.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Ministan yada labarai lokacin Mulkin Babangida, Janar Ukpo ya rasu
Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya na jMiyetti Allah MACBAN reshen jihar Malam Nura Abdullahi, ya zargi Yan kabilar Irigwe da fille wa wani bafulatani Kai Mai suna Musa Sale, tare da jikkata wani Mai suna Abdulssalam Nuhu lokacin da suke kiwon dabbobi a yankin Kwachudu.
Sai dai Yan kabilar Irigwe sun karyata wannan zargi, da Shugaban kungiyar Fulani ya ke mu su.
Kazalika awanni kadan bayan yai farmakin farko, sai aka tsinci gawar-wakin Mutum biyu na kabilar Irigwe a safiyar yau Litinin, a yankin Renwienku, dake karamar hukumar ta Bassa.
Inda Mai magana da yawun kungiyar Yan kabilar Irigwe Malison David, shima ya zargi Fulani da kai harin, inda suma kungiyar Fulanin suka karyata wannan zargi.
Wadannan tagwayen hare-hare na zuwa ne kwanaki biyar bayan bangarorin biyu sun yi wata ganawar sulhu da Gwamnan jihar Simon Lalong, domin samun dauwa-mammen zaman lafiya a jihar.
Sai dai harkawo hada wannan rahoton, Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ASP Ubah Gabriel, bai dauki waya ba, kuma bai amsa sakonnin kartakkwana ba da manema labarai suka tura mi shi.
Comments 1