By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato tace jami’anta sun kama mutane 12 tare da kwato babura 12, dangane da harin da aka kai da yammacin ranar Lahadi a kauyen Pinau, dake cikin masarautar Mavo na karamar hukumar Wase a jihar.
Rundunar a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Gabriel Ubah ya fitar tace: “A ranar 12/12/2021 da misalin karfe 16:30, mun samu kiran gaggawa wanda har yanzu ba a tantance ko su wanene ‘yan bindigar da suka kai hari kauyen Pinau ba.
Abin takaici, sun kashe mutane tara yayin da mutane hudu suka jikkata. Bayan samun rahoton ne aka hada tawagar ‘yan sanda, STF da sauran hukumomin tsaro, inda suka garzaya zuwa wurin da lamarin ya faru, inda aka cafke mutane takwas da ake zargi, an kuma kwato babura 12. Ana ci gaba da gudanar da bincike, da kuma ci gaba da kokarin kama wasu da ake zargi wadanda suka gudu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A halin da ake ciki yanzu an tsaurara matakan tsaro a yankin domin hana barkewar rikici.”
Da yake mayar da martani kan kamun, Gwamna Solomon Lalong a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Makut Macham ya fitar, ya yaba wa jami’an tsaro bisa “gaggauta matakin da suka dauka tare da bin diddigin maharan tare da ban kado maboyarsu, lamarin da ya kai ga cafke wasu da ake zargi.”
Sannan ya bukace su da su gudanar da kwakkwaran bincike domin bankado wadanda ke da hannu wajen kai hare-hare da kuma musabbabin harin, ya yi gargadin cewa “Gwamnatin Jihar Filato ba za ta bari masu aikata miyagun laifuka su yi katsalandan a kowane bangare na jihar da nufin tada zaune tsaye ba.”
Kazalika ya jajantawa wadanda harin ya rutsa da su, ya kuma umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar da kuma mahukuntan kananan hukumomi da su ziyarci yankin da kuma bayar da agaji ga wadanda suka tsira da rayukansu da kuma iyalan wadanda aka kashe.
A halin da ake ciki Gwamnan ya shawarci al’ummar Jihar Filato da su yi taka-tsan-tsan tare da kai rahoto ga jami’an tsaro da duk wani abu da suke da alaka dasu musamman a lokacin watan yulet don tabbatar da cewa ba a samu tabarbarewar zaman lafiya ba tare da tabbatar da cewa “gwamnati tana aiki da jami’an tsaro don tabbatar da isassun tura ma’aikata da kuma mayar da martani ga duk wani lamari.”