By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar dattawan Arewa ACF tace wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, Inda ta bayyana cewa hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa a matsayin ‘abin kunya ne a kasa.
Kungiyar ta dattawan Arewa ACF ta bakin sakataren yada labaranta na kasa Emmanuel Yawe, a wata sanarwa data fitar a Kaduna ranar Litinin, tace ci gaba da kai hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa ‘yan kasar ba abu ne wanda da za a amince da shiba.
A wani labarin kuma da ake ganin kamar yadda aka yi garkuwa da wasu matafiya tare da kashe wasu daga cikinsu, inda suka kashe tsohon dan tar takarar gwamna a jihar Zamfara, Alhaji Hamida Sagir a ranar Lahadin data gabata, kungiyar ta dattawan Arewa ta yi kira ga gwamnatin tarayya dana jihohi dasu kubutar da ‘yan Najeriya daga ‘yan ta’adda.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Kungiyar ta dattawan Arewa na kara tada jijiyoyin wuya sakamakon ayyukan ta’addancin da ba a kayyade ba a kan babbar hanyar Abuja, babban birnin tarayya da kuma Kaduna, tsohuwar hedikwatar rusasshiyar yankin Arewa.
“A kullum, ana ta’addancin ‘yan Nijeriya, ana garkuwa dasu, ana kashe su ba tare da barin su a wannan hanya ba. Wannan abin kunya ne na kasa kuma ba shi da karbuwa ga dandalinmu.
“Wanda wannan ta’addancin na baya-bayan nan ya rutsa da shi shine Alhaji Hamida Sagir, da darakta mai kula da ladabi na hukumar raya babban birnin tarayya FCDA kuma mai neman takarar gwamna a jihar Zamfara wanda aka harbe shi a Rijama.
“Hakika, Rijama ta zama wurin da ake yawan kai wadannan hare-haren ta’addanci a Yau da kullum.”sannan ya kara da cewa dole ne hukumomin tsaro su shawo kan kalubalen.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A halin da ake ciki, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdul Aziz Yari, ya yi alhinin rasuwar Sagir, wanda ‘yan bindiga suka kashe a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Gusau ranar Litinin mai dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Jam’iyyar APC ta Yari, Alhaji Ibrahim Magaji.