Majalisar dattawa a ranar laraba ta tilastawa kwamitin majalisar a kan harkokin kwastan bincikar kashe-kashen da jami’an kwastom suke a kan iyakokin kasar.
Hakan ya biyo bayan maganar da Sanata mai wakiltar Ogun ta yamma, Tolulope Odebiyi ya yi a zauren majalisa. Ya ce akwai bukatar a yi Allah wadai da abin da jami’an kwastan suke a yankin Idiroko da ke karamar Ipokia a jihar Ogun.
Da yake korafin, Odebiyi ya ce biyo bayan rufe bodar kasar da a ka yi, jami’an kwastan na abin da kare ma ba zai ci ba.
Da yake nuna goyon baya ga wannan korafin, sanata mai wakilatar Kwara ta tsakiya, Ibrahim Oloriegbe ya ce abin Allah wadai ne a ce kullum ana kashe ‘yan kasa. Mutanen da ya kamata su rika aikinsu sun je sun bige da kashe ‘yan kasa.
Shugaban majalisar ta dattawa, Sanata Ahmad Lawan da sauran ‘yan majalisar sun goyi bayan wannan kudurin.