Hukumar lura da kananan yara ta majalisar dinkin duniya wato UNICEF ta ce; kashi 49 na kananan yara ‘yan kasa da shekara biyar a Nijeriya ba sa samun kulawa yadda ya kamata shiyasa ma ba su girma da koshin lafiya. Inda ta ce ko sun girma suna girma ne a gajejjeru ko da kiba da sauran su.
UNICEF ta bayyana hakan ne a sanarwar da ta fitar, inda ta ce rashin samun abinci da ke gina jiki babban kalubale ne da bangaren lafiyar al’umma ke fuskanta. UNICEF ta ce shayar da yara kanana nono na ceton rayuwarsu, amma sun ce akwai takaici ta yadda kashi 27 ne na kananan yara kasa da wata shida zuwa shekara guda ake shayar da su yadda ya kamata.
Wanda suka kara da cewa; wannan yana nuna cewa; da yawan jariran da ake Haifa a Nijeriya suna fukantar matsalolin shayarwa da kuma amfana daga nonon iyayensu mata. Wanda suka ce nonon mahaifiyar ta su shi ne babban maganinsu da za su sha ya tseratar da rayuwarsu.
UNICEF ta yi gargadin cewa rashin samun abinci isasshe wanda yara ke fuskanta tun daga haihuwa, to hakan na shafar bunkasar kwakwalwarsu, da dakushe fahimtar karatunsu, da barazanar kamuwa da cututtuka tare da rashin samun kariya a jiki yadda ya kamata.
Da wannan suka yi kira ga gwamnati na kowanne sashe na kasarnan, da su yi kokarin magance wannan matsalar, inda kuma suka yi kira ga kamfanoni, kungiyoyi taimako da ‘yan kasuwa da iyayen da ma’aikatan lafiya da su tallafawa ire-iren wadannan yara.