By Ishaq Dabai
Sama da kashi 50 cikin 100 na matan Najeriya basa kan layi kuma ba tare da sun sami damar shiga shafukan sada zimunta na (Internet) ba, yayin da kashi 20 cikin 100 basu da yawa fiye da maza, sannan basa iya mallakar wayoyin komai da ruwanka, wanda ke haifar da gibin banbanci a tsakanin su, Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya koka da hakan a ranar Litinin.
Kungiyar ta kuma nuna damuwar ta kan yadda ‘yan mata matasa a Najeriya ke barin makaranta inda suka ce sun kiyasta sama da miliyan 1.3 ake samu a shekara.
Mataimakin Wakilin UNICEF a Najeriya, Rushnan Murzata,shine ya fadi wadannan a cikin wata gabatarwar da yayin ranar Yara mata ta Duniya ta shekara 2021 mai taken, wannan zamani.
Kungiyar tace ‘yan mata masu tasowa sun bar makaranta kafin su kai shekarar karshe ta karatun sakandare, a cewarta, hada zamani da kuma karatun zamani na da matukar mahimmanci ga walwala da nasara a matsayin iya karatu da rubutu.
Murzata yace, “Sama da‘ yan matan Najeriya miliyan 1.3 aka kiyasta zasu daina a kowace shekara kafin su kai shekarar karshe ta karatun sakandare.
“A kan samun zamani a ƙasashe masu ƙarancin kuɗi da matsakaita kamar Najeriya, sama da kashi 50 na mata basa hawa yanar gizo gizo, kuma mata sun ragu da kashi 20 cikin ɗari fiye da maza don mallakar wayar hannu. Haɗin zamani da karatun zamain na musamman yana zama mai mahimmanci ga walwala da nasara kamar ikon karatu da rubutu.
“Muna son amfani da damar bikin wannan shekarar don neman ingantacciyar hanyar samun fasahar zamani da sauran dabarun rayuwa ta ‘yan mata don canzawa zuwa karatun sakandare. Bari mu sanya ‘yan mata su zama masu bada shawara ga ilimin ‘yan mata da karatun zamani. “