Kashi na karshe na Alhazai 94 sun dawo Kaduna, yayin da Jihar ta kammala jigilar fasinjoji
Kashi na ƙarshe na kimanin Alhazai 94 da jami’ai da suka gudanar da aikin hajjin bana daga Kaduna sun dawo gida bayan shafe akalla makonni shida a Makkah da Madina, Saudi Arabia.
Sun isa filin jirgin sama na Kaduna ranar Lahadi da misalin karfe 9:37 na dare.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin PDP: Ba za mu bada ƙuri’un mu ga wanda suka tsani Jihar Ribas ba – Wike
Daily Trust ta ruwaito cewa, kimanin Alhazai 2,500 daga jihar ne kamfanin Azman Air ya yi jigilar su a rukunin bakwai daga filin jirgin.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kaduna, Alhaji Salisu Anchau, ya ce daga cikin wadanda aka dawo da su akwai Babban Sakataren Hukumar, Dakta Yusuf Yakubu Arigasiyyu; Darakta, gudanarwa da kudi, Hajiya Hannun Zailani, da daraktan ayyuka, Alhaji Alhassan Abubakar, da dai sauransu.
Da yake zantawa da Manema Labarai jim kadan bayan isowarsa filin jirgin sama na Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata, Shugaban Hukumar ya bayyana jin dadinsa bisa nasarar kammala aikin hajjin 2022.
Ya kuma yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Ya ba su damar yi wa al’umma hidima da kuma ba su rayuwa har zuwa karshe.
Idan za a iya tunawa, an fara jigilar maniyyatan ne a ranar 20 ga watan Yuni, 2022 tare da maniyyata 393 a cikin jirgin Azman Airbus A340-600 daga Igabi, Zariya, da Lere.