Darakta-Janar ta hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce sama da kashi 70 cikin 100 na kayan abinci da ake fitarwa daga Najeriya ana ƙin karbar su a kasashen waje.
Farfesa Adeyeye ta bayyana haka ne a wajen kaddamar da sabon ofishin NAFDAC na filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake a jihar Legas.
KU KARANTA: Kano: Hadakar Ƙungiyoyin Fulani Sun Sauke Tsohon Shugaban su
A cikin wata sanarwa da mai ba da shawara kan harkokin yada labarai a hukumar ta NAFDAC, Sayo Akintola, ya fitar a ranar Lahadi, Adeyeye ta ce matsalar kin fitar da abinci daga Najeriya a wasu kasashen Turai da Amurka na iya zama tarihi nan ba da jimawa ba, idan aka yi hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Hukumar da sauran hukumomin gwamnati a tashoshin jiragen ruwa sun karfafa ayyukan da suke domin tabbatar da komai ya tafiya yadda ya kamata.
Adeyeye ya ce, halin da ake ciki na saukaka kasuwancin fitar da kayayyaki da aka kayyade daga kasar nan na ci gaba da zama abin damuwa ga hukumar, inda ya kara da cewa ziyarar da hukumar ta NAFDAC ta ke yi na fitar da kayayyaki da ke cikin filin jirgin sama na kasa da kasa zai bayyana babban dalilin da ya sa ake ci gaba da kin amincewar hukumar.
Najeriya na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da dama, kuma kayan yawanci daga cikin wadanda ta kan samar ne.
Ta yi nuni da cewa, hukumar tana mayar da martani kan kalubalen da ake fuskanta ta hanyar hada kai da hukumomin da ke kula da tashoshin jiragen ruwa ta hanyar tabbatar da cewa kayayyaki sun cika ka’idojin kasashen da ake shigowa da su da kuma wuraren da ake shigowa da su.
Da take yabawa Hukumar Kwastam ta Najeriya, ta ce, idan babu kwastam, ba za su iya yin abubuwa da yawa da suke iya yi a yanzu ba.
Hakan kuwa tana tabbata ne da Haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kwastam da NAFDAC da sauran su.
A wani labarin kuma: Bazan Fasa Korar Gurbatattun Ma’aikata Da Ruguza Gine-ginen Ba,Har Karshen Mulki Na —El-Rufa’i
Gwamna Nasir El-Rufai ya sha wani alwashi na ci gaba da kakkabe duk wasu baragurbi a gwamnatin sa har zuwa lokacin barinsa mulki.
El-Rufai ya bayyana cewa ya jajirce wajen ci gaba da wannan yunkuri domin kada magajinsa ya sake yin hakan
Gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddaamar da wani littafi ranar Asabar, 20 ga watan Mayu