Kaso hudu ne kacal za su samu damar karbar bashi daga MSMEs
Duk da kokarin da babban bankin Najeriya ya ke yi don ganin ya baiwa masu karamin karfi jari don habbaka sana’ar su abun yaci tura.
Kaso hudu ne cikin mutane miliyan 40 suka cika sharuddan samun bashin da babban bankin zai bayar. Kamar yadda Jaridar Guardian ta ruwaito.
Karanta:-Kayi shiru kawai ka cigaba da aiki, Dare ke gayawa Rohr
Dr. Tunde Papoola yace hakan ya samo asali ne kan duba kudirorin masu karbar bashin da abun da zasuyi dashi.
Yace ” daga cikin abubuwan da ke kawo tsaiko wajan hana bashin sun hada da rashin tantance ko rubuta bayanai, rashin gabatar da kwakwkwaran tsarin kasuwanci da kuma rashin gabatar da abunda za’a karbi bashin dashi.”
Ya shawarci masu neman bashi dasu rinka rubuta bayanai akan harkokin kasuwanci su, sa’annan akwai hanyoyi da dama da mutane za su karbi bashi tun daga kan gwamnatoci, kamfanoni da sauran kungiyoyi masu zaman kansu.