Kananan ‘yan kasuwa da matsakaita na kokawa sakamakon yadda kasuwanci ke ci gaba da yin kasa saboda yadda aka kulle kasuwanni da killace al’umma a gida a wani mataki na gwamnati wajen ganin a dakile yaduwar cutar Coronavirus a Nijeriya.
‘Yan kasuwar sun shaidawa majiyarmu cewa; yanzu kam tabbas kasuwanci ya yi kasa sosai, kudade ba su shigowa, kuma wanda suka tara sun fara cinye su saboda rashin samun ribar kasuwanci da ba a yi yanzu.
‘Yan kasuwar sun tabbatar da cewa wannan cuta da ta yi zuwan ba zata ba tare da shiri ba, a daidai lokacin dama da kasuwanci ke samun koma baya, sun ce COVID-19 ta kara taimakawa wajen yiwa kasuwanci bugun karshe.