Majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan faduwar darajar naira.
Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Olubunmi Adetunmbi (APC, Ekiti ta Arewa) ya gabatar.
A halin yanzu dai Naira ana cinikinta tsakanin N690 zuwa N700 kan kowacce dala a kasuwar bayan fage.
DUBA WANNAN LABARIN: Ganduje Na Shirin Naɗa Sabbin Kwamishinoni
Da yake bayar da gudunmawa a muhawarar, sanata mai wakiltar Neja ta Gabas, Sani Musa, ya ce Naira za ta kara daraja idan aka cinye abin da aka noma.
A nata bangaren, Sanata mai wakiltar Ekiti ta Kudu, Biodun Olujimi, ta zargi CBN da daukar nauyin ganin Naira ta samu koma baya.
“Yawancin abin da ke faruwa shi ne saboda mutane suna fitar da dala suna sayar da su suna dawo da su – ya kamata mu ladabtar da faruwar hakan.”
“Lokaci ya yi da za mu duba gaba daya abin da ke faruwa. Abin da ke faruwa da dala, kwatankwacin abin da ke faruwa ne ga Najeriya.”
Majalisar dattawan ta bukaci babban bankin kasar da ya dakatar da faduwar darajar Naira cikin sauri.
JARIDAR DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa an amince da kudirin ne bayan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya kada kuri’ae amincewa da hakan.