An samu firgici a wani Katafaren Kanti na 7-eleven dake birnin Bangkok na Thailand bayan da wani Wagegen Kadangare ya yi tsallen badake ya faɗa Kantin.
A wani Faifan bidiyo da ya karade shafukan yanar gizo, an ji mutane na ta karagi da kuma dariya bayan da Ƙadangaren ya ɗale kan matakalan Kantin.
Al’amarin ya wakana ne a wani yanki mai suna Nakhon Pathom dake wajen birnin Bangkok.
Sai dai ba tare da wata-wata ba wani Ma’aikacin Kantin ya kirawo jami’an yan sanda inda suka sanya majanyi suka janye Wagegen Kadangaren da samun irin shi sai an tona.