Gwamnatin jihar Kaduna ta bukaci al’ummar jihar da shekarun su suka kai 18, kan su tabbatar sun mallaki katin zabensu kafin ranar 31 ga watan Yulin nan da muke ciki.
Baya ga haka, gwamnatin Kaduna ta kuma bayar da hutun ranaku biyu ga ma’aikatan jihar, domin suke su mallaki nasu katin.
Babban mai baiwa gwamnan Kaduna shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ne ya sanar da hakan a wata Sanarwa da ya rabawa manema labarai da yammacin yau Talata.
DUBA WANNAN LABARIN: NLC Ta Ayyana Tsunduma Yajin aikin gama gari
A cewar Muyiwa ranakun sune 27 da 28 ga watan Yuli, wanda hakan a cewar sa, zai basu damar zuwa Don Mallakar nasu katin.
JARIDAR DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa gwamnatin Kadunan ta kuma bukaci hukumar zaben wajen ganin ta yi abinda ya dace, don baiwa kowa damar ya mallaki nasa katin.
Gwamnatin ta kuma bukaci shugabanni a wurare daban daban, kan su umarci mabiyansu kan su mallaki nasu katin.