Wasu mata biyu ne suka rasa rayukansu sannan sama da gidaje 30 ne aka ce sun ruguza sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Asabar a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
A cewar wani jami’in yada labarai na karamar hukumar Abdulkarim Sani, daya daga cikin matan ta mutu ne bayan da bangon ginin nata ya ruguje ya fado mata. ya ce tun a lokacin an binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sani ya kuma bayyana cewa, al’ummar Nasarawa da Matsiga ne suka fi fama da bala’in ruwan sama da ya afku a tsakanin daran ranar Asabar da Lahadi.
Hukumomin yankin na ci gaba da kokarin tantance yawan barnar da ruwan yi wa mutane, gidaje da gonaki kamar yyaadda rahotonni suka bayyana.
Har yanzu dai Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ba ta fitar da wata sanarwa ko amsa tambayoyi kan lamarin ba.
A wani la Ari. Kuma na daban
Yan Bindiga Sun Sace Fastoci Uku A Jihar Kogi, Sun Bukaci Naira Miliyan 80 A MMatsayin kudin Fansa
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu fastoci uku a kan hanyar Ochadamu-Okele-Ejule a ranar Juma’a a karamar hukumar Ofu ta jihar, sun bukaci a biya su naira Milliyan 80 a matsayin kudin fansa.
Daily trust ta ruwaito cewa daya daga cikin wadanda da aka sace akwia Fasto Sunday Emmanuel Abbah daga karamar hukumar Olamaboro, Wanda yake zaune a Lokoja.
Fastocin uku an ce suna kan hanyarsu ne daga Lokoja domin yin hidima, hahin da ‘yan ta’adda a wata Suka farmake su a Wani yanki dake gabashin Jihar Kogi a lokacin da maharan suka tare motarsu a kusa da yankin Ochadamu zwa Okele-Ejule
Wata majiya daga daya daga cikin fastocin da aka sace ta ce masu garkuwar sun yi kira waya inda suka bukaci da a biya su Naira Milliyan 80 kafin a sako fastocin.
Sai dai rundunar Yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin na garkuwa da mutane, inda ta ce ta tura jami’anta zuwa domin ganin an sako mutanen.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar Yan sandan jihar, SP William Aya, “Rundunar ta na sane kuma tana kokarin ganin an sake su”.
Comments 1