Katsina: Ayarin Jami’an Tsaron Buhari basu wani yaƙi ƴan bindiga a lokacin Ƙwanton Ɓauna
Sabon bayani dake zuwa daga wasu Mazauna ƙauyukan Katsina dake kusa da inda aka yiwa Tawagar Shugaban Ƙasa Ƙwanton Ɓauna a ranar Talata, ya nuna cewa Jami’an tsaron Tawagar basu yi musayar wuta da ƴan bindiga ba, shiyasa Maharan suka tsere ba tare da komai ba.
Wani wanda ya shaidawa Daily Trust yace Maharan sun shiga wani ƙauye da ake kira Buturkai inda suka kori mazauna garin, suna masu tilasta mutane su koma ƙauyen Turare, inda harin ya afku, wasu kuma Shandai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Burtaniya: Karin Ministoci 7 Sun Yi Murabus Yayin Da Boris Johnson Yake Fuskantar Matsin Lambar Sauka Daga Mulki
Yace wannan lamarin ya faru ne kafin zuwa Tawagar Shugaban Ƙasa.
“A Buturkai, ƴan bindigar sun kashe mutane uku, sannan sun je Dogon Ruwa inda suka kashe mutane biyu, sun ɓalle Shaguna da dama, tare da tafiya da kayayyaki masu mahimmanci, kafin suje ƙauyen Marke, inda suka sace Dabbobi,” Inji shi.
Yace a lokacin da tawagar suka zo Turare, sun gano abinda ke faruwa, sai suka tsaya a Makarantar Firamare a ƙauyen na wani lokaci, sun yi bincike, sun cigaba da tafiyar su, a lokacin da suka cigaba da Harbe-Harbe a saman iska, har sai da suka wuce wurin mai hatsari.
Wani Mazaunin Marke, inda ƴan bindigar suke yace “bayan ƴan bindiga sun bar ƙauyen, sannan suka wuce.