By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanya ranakun 29 da 30 ga watan Oktoba domin gudanar da jarabawar gwajin a (CBT) a wani bangare na daukar aikin ‘yan sanda a jihar, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sanda SP Gambo Isah ya bayyanawa manema labarai, a ranar Litinin, a Katsina.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “An shirya gudanar da jarabawar ne a ranakun 29 da 30 ga watan Oktoba, 2021, a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da kuma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina daga karfe 8 na safe zuwa 3 na rana.
“Masu takara su duba imel ɗin su don samun takardar gayyata, wurin da kuma lokacin jarrabawar.
Ga wadanda basu samun sakwannin imel ba, ana ba su shawarar su kai rahoto zuwa hedikwatar ‘yan sandan Katsina, don bincika sunayensu,” in ji sanarwar.
07063977343