‘Yan bindiga a jihar Katsina sun ‘kama wani dan fashi da aka samu da kayan sata a wani kauye.
Mutumin mai matsakaicin shekaru ya kware wajen fitar da sandunan ƙarfe da kuma cire sandunan ƙarfe daga gine-ginen da mutane.
‘Yan fashin sun bayyana yadda suka kama wanda ake zargin a lokacin da suke sintiri a unguwar kan babura.
KARANTA ANAN: Tsaro: Yadda Yan Bindiga Sukan Tare Hanyar Birnin Gwari/Funtua
A cikin wani faifan bidiyo da kafar yada labarai ta PRNigeria ta samu, sun gabatar da shu’umin mutumin a gaban wani shugaban al’ummar yankin.
Ƴa. bindigar dauke da muggan makamai daban-daban, sun bukaci shugaban ya mika mai laifin gaba don ladabtar da shi.
A cewarsu laifin sata babban zunubi ne, don haka duk wanda yake ya tuba, domin kuwa zasu ci gaba da farautar irin wadannan bata gari.
A wani labarin kuma: Rikicin PDP: Wike ya yi barazanar yi wa makiyansa bulala a 2023
Yayin da rikicin cikin gida na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke ci gaba da yin ƙamari Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce zai yi wa makiyan sa na siyasa bulala mai ‘bakono’ a zaben 2023 mai zuwa.
Ya ce ba zai taba barin wani abu ga Allah ba.
Wike ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga shawarar da Gwamna Okezie Ikpeazu ya ba shi na ya bar duk wasu kura-kurai da ake yi masa na siyasa don Allah a lokacin da yake gudanar da wani aiki a jihar a Umuahia, babban birnin jihar Abia.