By Ishaq Dabai
Hukumar kwastam ta kafa wani kwamiti da zai binciki Harbin da akayi a cikin a yarin jerin gwanon kwamishinan na jihar Katsina yayin gudanar da aikinsu.
Jerin gwanon na kwamishinan kananan hukumomi da al’amuransu na jihar Katsina, Alhaji Umar Gwajo-Gwajo inda ake zargi wani jami’in hukumar kwastam yayi harbi a twagar ta kwamishina deke jihar Katsina.
Mr Dalha Wada-Chedi shine kwanturola na hukumar ta kwastom na jihar Katsina ya bayyana wa manema labarai cewa wannan kwamandan an kafa kwamitin binciken akan sa dan gane da faruwar hadarin.
Ana zargin jami’in kwaston din da harbi a jerin gwanon na kwamishinan a yayin gudanar da aikinsu akan hanyarsa ta dawowa daga karamar hukumar Daura zuwa gidan sa dake Mai-Adua.
Wada-Chedi ya bayyana cewa yana fata kwamitin zaiyi aikinsa bisa adalci, ya kara da cewa kwamitin da aka kafa za’a gabatar da shi ga jama’a da kuma daukar matakin daya dace.