Hukumar dale kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta ce kawo yanzu an samu ciro gawarwakin mutane 76 cikin mutane sama da 100 da hatsarin Jirgin ruwa ya ritsa da su kauyen Tsohuwr Labata dake karamar hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi.
Shugaban Hukumar a Jihar ta Kebbi Birma Yusuf shi ya bayyana haka a yau juma’a yayin tattaunawarsa da Jaridar Daily Trust.
Birma Yusuf ya kara da cewa yanzu haka ana chana ana vi gana da aikin ceto don gano karin wasu mutane da lamarin ya rutsa da su.
Ko da yake ya bayyana irin yadda ma’aikatan ceto ke iya kokarin su, to amma ya koka kan irin yadda karancin kayayyakin aiki ya jawo cikas wajen aikin nasu inda ya bukaci gwamnatin da ta dube su da idon Rahama.