Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya kaddamar da wasu kwamitoci guda 4, wadanda suke da alaka da tsaro domin kara inganta shi a jihar baki daya.
Kazalika an baiwa kwamitocin kayan aiki da suka haɗar da Mita kira Hilux guda 20, da kuma baburan hawa domin gudanar da ayyukan su guda 1,500.
Sakataren Gwamnan jihar Zamfara Jamilu Iliyasu Magaji ne ya sanar da hakan, cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai yau Talata.
Kwamitocin dai an raba su domin ayyuka daban daban, da suka haɗar da yaki da yan bindiga, da bayar da bayanai kan masu garkuwa da mutanan da sauran su.
Matawalle ya ce samar da kwamitocin wani bangare ne na kokarin gwamnatin sa wajen tabbatar da tsaron dukiya da rayukan al’ummar jihar.
Ya ce tun bayan Hawan mulki kawo yanzu yayi aiki da dama domin yaki da matsalar yan bindiga a jihar, dama sauran ayyukan bata gari baki daya.
Baya ga haka yace tuni ya samar da wurare da dama ga Fulani a jihar don zama, maimakon yawo da suke wanda hakan yake yawan haifar da rikici tsakanin su da manoma.