Kayi shiru kawai ka cigaba da aiki, Dare ke gayawa Rohr
Sunday Dare ministan wasanni da cigaban matasa na Najeriya ya gargadi mai horas da Yan wasan kwallon kafa na Najeriya kan irin yadda ya keyima Yan kwallon dake wasa a cikin gida.
Kamar yadda muka ruwaito muku mai horas da Super Eagles Rohr, ya zabi Austin Egouevoen a matsayin wanda zai horas da Yan wasan cikin gida, shi kuma an kawo shi ne don ya kula da babban kungiyar ta Super Eagles.
Karanta:-Sama da dalibai 42,000 ne basu karbi takardar shaidar kammala karatun na digirin su ba
Sunday Dare a lokacin da ya Ziyarci Yan kwallon a ranar Talata suna shirye-shiryen tafiya America don wasan sada zumunci da Kasar Mexico, yace “Rohr ka maida hankali akan aikin ka”. Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
Yanayin yadda yake nuna ko in kula ga Yan wasan gida Najeriya bai kamata ba, kuma wannan zai kawo ci baya ga kwallon kafa a kasar.
Ina kira ga Shugabannin kwallon kafa na Najeriya dasu ja hankalin sa, ya cigaba da aiki kamar yadda aka daukoshi yayi, ba surutu ba. Kamar yadda Sunday Dare yace.