Daga: Abbas Yakubu Yaura
Jagoran ‘yan adawa Raila Odinga, ya ce zai bi doka da tsarin mulki domin yin takara da sakamakon zaben shugaban kasa da aka kammala kwanan nan a Kenya.
Odinga, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Azimio La Umoja (Declaration of Unity) Kenya Alliance One, ya sha kaye a hannun mataimakin shugaban kasar William Ruto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwankwaso Ne Zai Gaji Kujerar Shugaba Buhari A 2023 – Cewar Jigo A NNPP
Ruto wanda a hukumance aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar litinin ya samu kashi 50.49 na kuri’un da aka kada inda Odinga ya samu kashi 48.5.
Kalaman na Odinga na farko kan sakamakon ya zo ne jim kadan bayan hudu daga cikin kwamishinonin zabe bakwai sun ce sun tsaya tsayin daka kan matakin da suka dauka kwana daya da ya gabata na yin watsi da sakamakon zaben shugaban kasar.
“Yana mai cewa tsarin tattara sakamakon zaben ya kasance a bayyane.”
“Ra’ayinmu shi ne alkaluman da shugaban hukumar zabe Wafula] Chebukati ya bayyana ba su da tushe balle makama kuma dole ne kotu ta soke shi.”
“Abin da muka gani jiya (Litinin) zalunci ne da kuma rashin mutunta kundin tsarin mulki da dokokin Kenya,” in ji shi.
Odinga ya ce “Za a bi dukkan tsarin mulki da na zabe da kuma na doka da muke da su.”
Ana sa ran Odinga zai daukaka kara a kotun kolin Kenya.