Kasar Kenya ta dakatar da dukkan jiragen fasinja masu shigowa da kuma jigilar fasinjoji daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) don ramuwar gayya kan matakin da Dubai ta dauka na haramtawa duk wani jirgin fasinja daga Kenya saboda gwajin Covid-19 na bogi.
Darakta Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kenya (KCAA), Gilbert Kibe ne, ya shaidawa jaridar EastAfrican a yau Talata cewa, dakatarwar ta fara aiki ne a ranar Litinin da tsakar dare na tsawon kwanaki bakwai.
Sai dai dokar hana zirga-zirgar ba ta shafi zirga-zirgar jiragen dakon kaya da aka saba yi da su ba, kamar Kenya Airways da Emirates airline daga UEA zuwa Kenya.
“An dakatar da zirga-zirgar fasinja masu shigowa da jigilar fasinjoji daga Hadaddiyar Daular Larabawa na tsawon kwanaki bakwai. Muna yin haka ne domin mayar da martani ga dokar hana zirga-zirgar fasinjojin Kenya zuwa UAE,” in ji Mista Kibe a yau Talata.
Haramcin ya zo ne ‘yan kwanaki kadan bayan UAE ta tsawaita dokar hana zirga-zirgar jiragen sama na Kenya bayan da ta tabbatar da cewa matafiya daga Nairobi suna samun gwaji mai ingancin Covid-19 bayan sun isa kasar Gabas ta Tsakiya, duk da cewa suna dauke da sakamakon gwaji mara kyau.
Babban darektan KCAA Gilbert Kibe ya ce shirin ya ƙunshi ɓangarorin cibiyoyin gwajin lafiya masu zaman kansu waɗanda suka haɗa kai da matafiya don ba da sakamakon Covid-19 na jabun PCR, don taimakawa tafiyarsu zuwa Dubai.