Shahararren ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City kuma ɗan asalin ƙasar Belgium wato Kevin De Bruyne ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila wato kakar wasan da aka kammala ta 2019 zuwa 2020.
De Bruyne dai ya doke abokan takarar sa wato ‘yan wasa guda biyar da suka haɗar da Sadio Mane da Virgil van Dijk da Trent Alexander-Arnold da Henderson dukkanininsu daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool da kuma ɗan wasan da suke fafata wasa tare da shi a Manchester City Raheem Starling.
De Bruyne dai shine ɗan wasan da yafi taimakawa aci ƙwallaye inda ya taimaka har sau 20 baya da ƙwallayen da ya dinga zazzagawa a zare shima, sannan kuma ya taimakawa Manchester City tazo matsayi na biyu a gasar ta ajin Firimiya ta ƙasar Ingila, haka zalika ya taras da tarihin da tsohon ɗan wasan Arsenal ya kafa na yawan taimakawa a jefa ƙwallaye a kakar wasa guda 1 wato Thierry Henry.
Haka zalika da taimakon Kevin De Bruyne Manchester City ta zura ƙwallaye guda 102 a gasar ajin Firimiya ta bana duba da cewar ba’a kowanne League aka sami wadda ta kaita zura ƙwallaye ba idan a kayi duba da sauran gasoshin Laliga da Serea A da Bundes Liga da kuma gasar nan ta French League 1.
Nan da wasu ‘yan makonni ake sa ran sake dawowa domin ci gaba da fara fafata sabuwar kakar wasa fil a leda wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 wato gasar Firimiya ta ƙasar Ingila kenan.