Ɗan wasan tsakiyar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City dake ƙasar Ingila kuma ɗan asalin ƙasar Belgium wato Kevin De Bruyne ya sake lashe wata gagarumar kyautar, ya lashe kyautar ne bayan hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar turai ta ayyana subansa a matsayin ɗan wasan da yafi kowa nuna bajinta a dukkanin ‘yan wasan tsakiya da ake dasu a manyan league na nahiyar turai.
Kevin De Bruyne dai ya fafata wasanni sosai a sauran ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa amma sai dai bata fashemasa ba kamar lokacin da ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City wanda a shekarun baya ya zauna a Chelsea a ƙarƙashin jagorancin mai horas wa Jose Mourinho inda suka sayar dashi.
Koda a kakar data gabata ta ajin Fitlrimiyar ƙasar Ingila De Bruyne yayi bajintar da a ‘yan wasan yanzu da suke fafata gasar babu wanda yayi irin bajintar da yayi inda sai da ya taimaka aka jefa ƙwallaye sau 20 inda ya kamo tarihin da tsohon ɗan wasan Arsenal kama ɗan asalin ƙasar Faransa wato Thierry Henry a shekarun baya a gasar ta Firimiya. Sannan kuma ya jefa ƙwallaye sosai a kakar wasan ta bata.
Wannan kyauta daya lashe bata rasa nasaba da irin bajintar da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Manchester City tayi a gasar zakarun nahiyar turai wato kakar wasan data gabata wadda ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta zamo zakara, inda shi kansa De Bruyne ya baiwa Manchester City gudun mawar data kamata, kama tun daga wasannin rukuni da kuma wasan da suka lashe ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid gida da waje, haka zalika ya nuna bajinta sosai a wasan da Manchester City tasha kashe a wasan kusa dana kusa dana ƙarshe inda Lyon ta caskarasu daci 3 da 1 wasan da aka sanya mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Manchester City tsugunan gwanan jaki.
Amma duk da cewar Manchester City an korota a iya wasan kusa dana kusa dana ƙarshe na gasar zakarun nahiyar turai hukumar ta duba taga babu wanda ya cancanci ya zamo gwarzon ‘yan wasan tsakiyar na nahiyar turai kamar Kevin De Bruyne duba da cewar babu wanda yayi bajintar da yayi a kakar wasan data gabata kuma aka duba aka ga ya cancanta.
Sai dai bayar da irin wannan kyautar ga ‘yan wasan da suke buga wasa a tsakiya a dukkanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasar Ingila ya zama sabon abu, duba da cewar mafi yawan irin kyaututtukan ana ‘yan wasan da sukafi lashewa suna masu fafata wasa a gasar Laliga, haka ba a fiye bayar wa a ‘yan wasan da suke buga wasa a gasar Serea A ba kokuma gasar Bundes Liga. Koda kyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya kokuma kyautar Ballon d’ Or ‘yan wasan da suke fafata gasar Laliga sunfi lashe wa.
Haka zalika tunda aka fara bayar da wannan kyauta ta gwarzon ɗan wasan tsakiya na nahiyar turai ‘yan wasa guda uku ne kacan suka taɓa lashe wa wato wadda Kevin De Bruyne ya lashe itace cikon ta uku inda abin yana ta baiwa mutane mamaki ganin cewar yadda ake gumurzu a gasar ajin Firimiyar ƙasar Ingila amma ‘yan wasan tsakiya basu fiye lashe kyautar gwarzon ɗan wasan tsakiya na turai ba.
Sauran ‘yan wasan tsakiya guda biyu da suka lashe wannan kyautar a ƙasar Ingila a shekarun baya sune David Beckham da kuma Frank Lampard wanda dukkaninsu sun ajiye takalmansa kuma kowannensu horas wa yakeyi, inda Beckham ya ƙasar Amurka yayin da Lampard shine mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea a halin yanzu.